Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Edo Ta kame Mabarata Ranar Jajibirin Sallah


Wadannan mabaratan sun hada da makafi guragu maza da mata

Gwamnatin jihar Edo dake kudancin Najeriya ta kame wasu daruruwan mabarata dake bara a birnin Benin gwamnatin jihar dai ta tsare mabaratan ne tun cikin watan azumin da yagabata kusan yau kimaninwata daya Kenan da ake tsare dasu.

Wadannan mabaratan sun hada da makafi guragu maza da mata, wannan yasa Muryar Amurka ta tunbtubi wadannan bayin ALLAH da ake tsare dasu domin jin halin da suke ciki. Ga dai mutum na farko

‘’Sunana Amadu ina cikin mutanen farko da aka kama, wallahi ba wanda ya taba bayyana muna cewa mu bar bara mu dai da Magariba zamu shiga cikin gida muyi buda baki kawi sai muka wasu jamiaai da motoci guda ukku sun kama mu sun dankara mu cikin motocin sun kawo mu nan, a ranar da suka kawo mu, a ranar da suka kawo mu ba wanda yakai abinci bakin sa har gari ya waye sailin nan kuma aka sake wuni cikin azumin nan haka muka wuni muka kuma sake daukar azumi sai da magariba tayi ne suka kawo muna shinkafa.’’

Shima wannan dan talikin ga abinda yake cewa.

Gwamnatin Jihar Edo Ta kame Mabarata Ranar Jajibirin Sallah - 3'27"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:27 0:00

‘’Gaskiya kaga wannan ramadana mun fara cikin farin ciki amma daga karshe bamu ji dadin sa ba , tunda anyi hawan idi kowa na murna su suna can da ‘ya’yan su, suna murna sunsa sabin kaya muko gamu nan kayan da muke ciki sai wari muke yi, ba wanka ba kome kuma yayan mu suna gida sai kuka suke yi.’’

Ga Lamido Abubakar da cikakken rahoton

XS
SM
MD
LG