Bayan batun cin hanci da rashawa da uwa uba yaki da kungiyar boko haram, shugabannin na Amurka da Najeriya zasu duba batun saka jari a wasu bangarorin tattalin arzikin kasa, bayan wanda aka san kasashen biyu tun farko akai wato cinikin man fetur wanda yayi kasa a halin da ake ciki.
Ko ina muhimmacin wannan ziyara musammam ga Najeriya,? ga dai abinda wani tsohon dalibi kuma malamin jamiaa a kasar ta Amurka Dr Danlami Alasan ke cewa.
‘’Kwarai akwai alfanu yakamata a fahinci cewa dai na daya Amurka din nan ita ce tattalin arzikin ta yafi ta kowace kasa karfi a duniya, na biyu kuma su wadancan abubuwa biyu da ka fada tun farko, wato taadanci da yaki da cin hanci da rashawa ba wanda zai tinkare su a duniya yayinasara cikinkwanciyar hankali da tsanaki sai kabi ta wata hanya ka sasanta da Amurka ka nemi gudun mowar su da taimakon su, karshen kiyayya da Amurka dai ita ce Iran, Yau ga iran nan tayi hankuri yarjejeniya na sulhu na fahintar juna da ita da Amurka, don haka ba karamin alfanu bane da muhimmamci na zuwan Shugaba mUhammadu Buhari Amurka musammam tun da shi shugaba Barrack Obama shine da kansa ya gayyace shi yazo wannan kasar’’
To sai duk da dinbin muhimmacin wannan ziyarar yanzu haka akwaii wasu yan kasar musammam yan jamiyyun adawa dake kushe ziyarce-ziyarcen da shugaban ke kaiwa kasashen ketare kasa da watanni biyu baya darewar sa kan karagar mulki.
Ga dai wani dan taliki mai irin wannan raayin da abinda yake cewa.
‘’Kamata yayi ace shugaban mu ya zauna gida sabo da kasar mu tana bukatar sabo da matsalolin da muke fama dasu musammam na tsarop sai kara taazzara suke yi, da akce ya nada ministoci wadanda zasu rika wakiltar sa a wasu abubuwa da hakan yayi dama-dama.
To sai dai duk da wannan kushe, mutane irin su Akitec Kabiru Ahmed wanda jigo ne a jamiyyar APC anan jihar Lagos yace ziyarar da shugaba Muhammadu Buhari yakai kasar ta Amurka domin ganawa da shugaba Barrack Obama nada muhimmacin gaske wajen tabbatar da tsaro da kuma ci gaban kasa, ga dai Akitec din da abinda yake cewa.
‘’Ato wannan ai matsalar su ce idan wasu sunyi suka mu dai mun san irin dinbin muhimmacin da wannan ziyara ta shugaba Buhari take dashi a kasar Amurka.Ina ganin tunda aka fara demokaradiyya a Najeriya kasashen turai basu taba haduwa sunce wa Najeriya ta kawo bukatun ta ba sai wannan karon, saboda haka shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tafi Amurka da bukatun yan Najeriya, wannan babban hubbasa ne kuma irin yadda kasashen duniya suke ganin wannan gwamnati tamu ta yanzu da mutunci da daraja da martaba yasa suma suka bude akalar su cewa me Najeriya ke bukata, me Najeriya keso ayi mata, sannan kuma ace zamu je mukaanta musu muna bukatar kaza muna bukatar kaza, a kasar da biyan albashin maaikata ya gagari gwamnatin PDP a Najeriyan nan, sannan kasashen duniya su hadu suce me kuke bukata kuzo muyi muku, sannan muce ba zamu je ba, sannanace wannan zuwa bashi da muhimmaci, idan mai fadan Magana wawa ne to kar mai fadan ta ya zama wawa’’
Kome ake ciki dai fatar yan Najeriya shine wannan ziyarar ta taimaka wajen kwato miliyoyin dalolin da ake zargin masu rike da madafan iko da suka kai ajiya kasar ta Amurka da sauran kasashen turai da kuma gano bakin warware zaren matsalar boko haram da ya addabi kasar musammam arewaci walawa.
Ga Babangida Jibrin Da cikakken rahoton.