Tsohon Jakada Yaro Yusuf Mamman, wanda yake tsokaci kan ziyarar aiki da shugaba Muhammadu Buhari, zai fara lahadin nan anan Amurka, yace ganin cewa Amurka ce jigo ta fuskar salon mulkin demokuradiyya, gayyatar da ta yiwa shugaba Buhari, alama ce ta kwarin guiwar da Amurka take da ita kan yadda Najeriya take tafiyar da wannan tsari.
Ya kara da cewa ganin yadda aka yi zabe lamin lafiya, kuma jam'iyya mai hamayya ta sami nasara, wannan yana karfafawa Amurka guiwa, take son ganin Najeriya ta zurfafa tsarin ya kafu sosai.
Wannan mataki a ganinsa zai taimaka wajen daidaita al'amura cikin kasa.
Ambasada Yaro Yusuf Mamman, yayi magana kan irin rawar da Amurka ta taka wajen yakin neman 'yanci kai daga hanun turawan mulkin mallaka, ta irin horo da tsohon shugaban Najeriya na jeka-na-yika, Dr. Nmamdi Azikwe, wanda anan Amurka yayi karatu ya koyo salon gwagwarmaya, ya koma yayi amfani da ita wajen jagoran kwatowa Najeriya 'yancinta daga turawan Ingilishi.
A nasa bangaren, tsohon jakadan Najeriya a Amurka Farfessa Jibril Amin, yace a harkar dangantaka tsakanin kasashe, abu ne da bashi da tabbas, yau da dadi gobe babu dadi.
Farfesa Aminu yana amsa tambaya ne kan ko ana iya sa ran hulda zata inganta tsakanin Najeriya da Amurka, ganin yadda dangantaka tayi tsami a zamanin gwamnatin shugaba Jonathan.