Alhaji Garba Umar yace wadannan jirage zasu taimaka gaya wajen samar da sufurin jiragen sama ga al'ummar jihar Taraba, sannan zasu kara irin kudaden shigar da gwamnatin jihar zata rika samu.
Mukaddashin gwamnan yace yayiu tattaki da kansa zuwa kamfanin da ya sayarwa da jihar Taraba wadannan jirage, kuma ya samu ragin tsabar kudi dala dubu 500, kimanin Naira miliyan 80.
Haka kuma, wata cibiya mai zaman kanta, Transparency Network, ta zabi mukaddashin gwamnan na Jihar Taraba, ta mika masa lambar yabonta a matsayin gwamnan da ya fi rike amanar kudaden jama'a da aka dora masa alhakin kulawa da su.
Alhaji Garba Umar ya tattauna da wakilin Muryar Amurka, Nasiru Adamu Elhikaya a lokacin da ya halarci taron bayar da lambar yabo ta kasa a Abuja.