Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Furucin Donald Trump Ya Kara Tsanani Kan Koriya Ta Arewa


Shugaban Amurka Donald Trump ya kara tsananta furucinsa kan kasar Koriya ta Arewa game da barazanar da ta yiwa Amurka.

Shugaban Amurka Donald Trump ya dada tsananta matsayinsa kan Koriya Ta Arewa jiya Alhamis, ya na mai cewa muddIn Koriya Ta Arewar ta takalo yaki, to fa, a ta bakinsa, "Sai sun ga abin da ba su taba tsammanin ya na iya faruwa gare su ba."

Trump ya ce watakila ma gargadinsa na farko, inda ya yi barazanar babbake kasar ta ‘yan kwamines da wuta mai azaba, saboda shirinta na nukiliya, watakila tsananin kashedin bai ma kai yadda ya kamata ba.

Da aka tambaye shi ko wani irin kashedi kuma zai fi na farkon tsanani, sai Trump ya fadawa manema labarai cewa, “Za ku gani … ya kamata Koriya Ta Arewa ta shiga taitayinta, idan ba haka ba za ta shiga irin rigimar da kasashen duniya kalilan ne kadai su ka taba shiga.”

Trump ya yi Magana ne ‘yan sa’o’i bayan da Koriya Ta Arewa ta ce ta na gab da kammala shirye-shiryen kaddamar da hare-haren makamai masu linzami guda hudu kan ruwayen da ke daura da gabar yankin Tsibirin Guam mallakin kasar Amurka, wanda shi ne na baya-bayan nan a takalar da Koriya Ta Arewa ta ke yi, a cacar bakarta da Amurka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG