Rundunar sojan Amurka tace ta hakura, zata watsar da kokarin da take na neman sojojin Amurka guda uku da suka salwance bayan da jirgin samansu ya fadi a cikin teku a kasar Australia jiya Asabar.
An dai ci sa’ar tsamo sauran sojojin kundumbala 23 dake cikin wannan jirgin samfurin MV-22 Osprey da ya abka cikin tekun.
Sanarwar da rundunar sojan kundumabalar suka bada tace yanzu ba neman wadancan sojan ukku suke ba, suna neman gawwawakinsu ne kuma tuni ma an riga an sanarda iyalansu abin da ya faru.
Sanarwar tace daga wani makeken jirgin ruwa mai jigilar jiragen sama ne aka aika jirgin da ya fadi ne zuwa aiyukkan shawagin da aka saba alokacin da wannan hatsarin ya auku.
Shima shugaban Amurka Donald Trump da yanzu ya soma hutu a garin Bedminster na jihar NJ, an sanar da shi game da faduwar wannan jirgin.
Facebook Forum