Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Bada Sharadin Tattaunawa Da Koriya Ta Arewa


Rex Tillerson
Rex Tillerson

Sakataren ma’aikatar harkokin wajen Amurka Rex Tillerson ya bayyana yau Litinin cewa, matakin da yafi dacewa Koriya ta Arewa ta dauka da zai nuna cewa, a shirye take ta koma teburin tattaunawa shine ta daina gwajin makamai masu linzami.

Bamu sani wani lokaci mai tsawo da bata dauki wani matakin takala ta wajen gwajin makamai masu linzami ba. Saboda haka, ina jin wannan ce alama mai karfi da zasu iya aika mana,su daina gwajin makamai masu linzami.

Ya bayyana haka ne a Manila, inda take halartar taron dandalin kungiyar kasashen yankin asiya -ASEAN.

Tillerson ya fada ranar asabar cewa, kwamitin sulhu na MDD ya kada kuri’a da ta sami cikakken goyon baya, na kakabawa Koriya ta Arewa sababbin takunkumi sabili da gwajin majamai masu linzami masu cin dogon zango, da nufin, aikawa kasar sako karara cewa, al’ummar kasa da kasa baki daya ba zasu lamunci matakan da Koriya ta Arewan ke dauka ba. Kuma abinda ake bukatar gani shine raba yankin Koriya da makaman nukiliya.

Koriya ta Arewa tayi allah wadai da takunkumin a wata sanarwa da ta fitar yau Litinin da aka yayata a kafar sadarwar kasar, ta kuma yi alkawarin daukar fansa kan Amurka tare da harba makamai masu linzami “ninkin-ba-ninki”, ta kuma jadada cewa, takunkumi ba za a tursasa mata da takunkumi ta koma teburin tattaunawa kan ayyukan nukiliya ba.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG