Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Korea ta Arewa Ta Yi Wancakali Da Barazanar Trump


Ministan harkokin wajen Korea ta arewa, Ri Yong Ho a lokacin da ya halarci wani taro ministocin kungiyar ASEAN a Manilla. (AP Photo/Aaron Favila)
Ministan harkokin wajen Korea ta arewa, Ri Yong Ho a lokacin da ya halarci wani taro ministocin kungiyar ASEAN a Manilla. (AP Photo/Aaron Favila)

Bayan zafafan kalaman da shugaban Amurka ya furta akan Korea ta arewa dangane da barazanar da take yi wa kasarsa, Korea ta arewan ta yi wancakali da kalaman na Donald Trump inda ta ce ba zai iya aiwatar da abinda ya fada ba.

Korea ta arewa ta yi watsi da gargadin da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi mata na cewa zai dauki matakin soji akan kasar, idan har ta ci gaba da yi wa Amurkan barazana.

A ranar Talatar da ta gabata shugaba Trump ya shammaci masu adawa da shi da magoya bayansa a gida da waje, tare da shan alwashin kai hari akan Korea ta arewa, inda ya yi amfani da zafafaan kalamai da wasu ke suka.

Trump ya bayyana cewa kasar ta Korea ta arewa za ta fuskanci "ukubu da luguden wuta," muddin ba ta fita hanyar Amurka ba.

Sai dai Janar Kim Rak Gyom, wanda shi ne kwamandan tsare-tsare na rundunar da ke sarrafa makaman roka, ya fadawa kamfanin dillancin labaran Korea ta arewa na KCNA a yau Alhamis cewa, kalaman na Trump duk ashana ne, domin ba abinda zai iya aiwatarwa ba ne.

A jiya Laraba, sakataren tsaron Amurka, Jim Mattis, ya ce Korea ta arewa na iya fuskantar barazanar a daidaita ta, idan har ta haddasa yaki, ya kuma yi kira ga hukumomin kasar da su yi watsi da shirinsu na mallakar makamin nukiliya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG