Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rex Tillerson Yace Bai Ga Wata Barazanar Tabbas Da Koriya Ta Arewa Ke Yiwa Guam Ba


Rex Tillerson-Sakataren Harkokin wajen Amurka
Rex Tillerson-Sakataren Harkokin wajen Amurka

Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson yace shi bai ga wata barazanar tabbas da Korea ta Arewa ke yiwa yankin Guam dake tsibirin Pacific ba, duk da ikirarin Pyongyang din cewar tana gwajin dabarunta na lullube wannan yanki na Amurka baki dayansa da wuta.

Tillerson ya zanta da manema labarai yayin da zai tashi zuwa yankin na Guam da safiyar yau Laraba biyo bayan zazzafar cacar baki tsakanin Washington da Pyongyang. Sakataren harkokin wajen Amurkan ya yada zango domin jirginsa ya sha mai a tsibirin bayan ziyararsa ta Asia.


Shugaban Amurka Donald Trump ya aike da kashedi mai karfi ga Korea ta Arewa, yana cewar idan ta ci gaba da yin barazana ga Amurka zata huskanci wuta da fushi mai tsanani da ba a taba gani ba a duniya.


Tillerson yace yana ganin shugaban ya aike da sakon ne da irin kalaman da shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Un zai fahimta, tun da yake baya fahimtar kalamun lumana ta diplomasiya.

Yace yana ganin shugaban Amurka yana kokarin ya fahimtar da gwamnatin Korea ta Arewa cewar Amurka karfin da babu tambaba da zata iya kare kanta da kawayenta kuma yace ina tunani cewar yana da muhimmanci ya aike da wannan sakon don kawo karshen bahagon tunanin da suke yi.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG