Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

France: An Kama Wanda Ake Zargi da Kai Hari Kan Kamfanin Man Gas


'Yansanda sun taru a kamfanin man gas da aka kaiwa hari a Faransa wanda mallakar Amurka ne
'Yansanda sun taru a kamfanin man gas da aka kaiwa hari a Faransa wanda mallakar Amurka ne

Shugaban kasar Faransa, Francois Hollande yace an kame wani mutum da ake zargi dahannu wajen kai hari akan wani kamfanin sarrafa Man Gas, inda mutum daya ya rasa ransa a kudu maso gabashin kasar.

An kai harin ne a yau Juma’a a birnin Lyon dake kudu maso gabashin kasar. An samu filallen kan mutum makalle a jikin kofar shiga kamfanin like da wata tuta mai rubutun Arabiya jiki.

Mr. Oland yace, “ wannan harin ta’addanci ne, babu makawa.”Yana furucin ne a wasu tashoshin telebijin na birnin Brussel, jim kadan kafin ya fita daga taron kolin kungiyar kasashen Turai.

Yayin da har yanzu dai babu wasu bayanai, shugaban dai yace a kalla wasu mutane biyu sun raunata a dalilin harin, wanda ya faru karfe goma na safiyar yau. Ya kuma ce an kwashe duk ma’aikatan kamfanin da ‘kara karfin matakan tsaro a kamfanin.

Wasu shaidu daga kamfanin sunce maharin ya tuko mota cikin kamfanin ya kuma tada bom, kuma har yanzu ba’a san ko akwai hannun wasu cikin wannan hari ba.

XS
SM
MD
LG