A yau Laraba ofishin Mr Hollande ya fitar da wata rubutacciyar sanarwa, bayan da shugaban ya gana da wasu manyan hafsoshin tsaronsa, kan rahoton da Wikileaks mai kwarmata bayanan sirri ya fitar na wasu takardun da suka nuna cewa Hukumar Tsaron Amurka ta NSA, ta tatsi bayanan shugabannin Faransa biyu da suka gabata da na Hollande.
Jami’an gwamnatin Faransa sun tabbatar da cewa an gayyaci Jakadan Faransa da ke Amurka, zuwa ofishin ministan ma’aikatar harkokin wajen Faransa Laurent Fabius, domin tattauna wannna batu.
Bayanan na Wikilieaks an wallafa su ne a wata jaridar Faransa da ake bugawa a kowace rana mai suna Liberation da kuma shafin intanet dinnan dake binciken kwakwaf, da ake kira Mediapart.
Ya zuwa yanzu babu tabbacin sahihancin wadannan rahotanni.
Fadar Shugaban kasar Amurka ta White House ba ta yi cikakken bayani game da wannan zargi ba, sai dai ta jaddada cewa ba ta tsati bayanan shugabannin na Faransa ba, kuma ba tadaniyyar aikata hakan,