An fara harin ne da wata gagarumar fashewa wani bom a babbar kofar shiga harabar majalisar. Wasu fashe fashe da suka biyo ba sun sa anga hayaki na tashi daga ginin, lamarin da ya sa hayakin ya turnuke har cikin ginin, yayinda 'yan majalisa suka tsere cikin tsoro.
Wani kakakin ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar yace mayakan Taliban su bakwai wadanda suka yi damara da nakiyoyi suna daga cikin wadanda suka kai harin, kuma dukkansu jami'an tsaro sun kashe su, wanda ya kawo karshen kawanyar da aka yiwa majalisar na kusan sa'o'i biyu.
Ma'aiktar tace babu wakilin majalisa da ya jikkata sakamakon harin, amma jami'an kasar suka ce akalla wasu mutane 30 sun jikkata, cikinsu harda mata biyar da yara uku, wasu raunukan da suka samu suna da tsanani.
Ofishin jakadancin Amurka dake Kabul ya fidda sanarwa inda yayi Allah wadai da harin, yana cewa "kai hari kan majalisa ya nuna a fili rashin mutunta tsarin Demokuradiyya da doka da Oda"