Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Texas: Wanda Ya Zana Siffar Manzon Allah (SAW) Ya Gurfana Gaban Kotu


Adul Malik Abdul Kareem mutumin da ake zargi da zana siffar Manzon Allah (SAW)
Adul Malik Abdul Kareem mutumin da ake zargi da zana siffar Manzon Allah (SAW)

A jiya Talata ne wani mutum da ake zargi da laifin kulla makarkashiyar harin da aka kai akan masu gudanarda gwaje-gwajen zane-zanen siffar Manzon Allah, Annabi Muhammad (SAW) a jihar Texas, ya bayyana a gaban wata kotun tarayya.

Tun cikin makon jiya ne dai aka cafke wannan mutumen mai suna Abdul Malik Kareem a birnin Phoenix (Fee-nix) na jihar Arizona. Takardun da aka gabatar a kotun sunce tun farkon watan Janairun wannan shekarar ne Kareem ya sauke ‘yan bindiga biyu a gidansa, watau Elton Simson da Nadir Soofi, inda kuma a lokacin ne suka kitsa yadda zasu kai harin.

An kuma zarge shi da samarda makaman da Soofi da Simson suka yi anfani da su wajen kai farmakin da kuma shata karya a bayanan da ya baiwa jami’an tsaro na tarayya. Simson da Soofi dai, wadanda ke zaune a gida guda, sun tuka mota ne zuwa garin Garland dake jihar Texas inda suka bude wuta akan taron masu gwaje-gwajen zanukkan Annabi din , har suka raunana wani mai gadi, amma su kuma anan ‘yansandan Garland suka bindige su har Lahira. Kareem dai ya musanta zargin kuma alkalin kotun ya bada umurnin a ci gaba da tsare shi ba tareda an bada belinsa ba.

VOA60 DUNIYA: Gangarumin Zanga Zanga A Amurka, Afrilu 28, 2015
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:00 0:00

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG