Kamfanin Airbus, Siemens da kamfanin Rolls-Royce, masu kera motocin alfarma, na wani yunkuri na kera jirgin sama mai amfani da hasken rana. Jirgin wanda za’a yi shi dauke da farfela guda daya.
A bangare daya na jirgin za’a samar da wasu kananan ingina guda uku masu amfani da mai, don gudun bacin rana, a duk lokacin da babban injin jirgin ya samu wata matsala jirgin ba zai tsaya ba, da taimakon kananan inginan uku.
Wannan yunkurin nasu, yayi dai-dai da zamanin da ake ciki, na cigaban kimiyya da fasaha, musamman idan akayi la’akari da yadda, ake kara samu yawaitar karuwar gurbatar yanayi a fadin duniya. Wanda hakan yake haddasa hauhawar dumaman yanayi.
Hakan zai taimaka matuka, wajen raguwar dogaro da akeyi na amfani da mai a jiragen sama, wanda hakan ke taimakawa matuka wajen gurbatar yanayi. Kamfanonin uku a ranar talata, suka bayyanar da kudurin su, na daukar alwashin kera jirgi samfurin E-Fan X, nan da shekarar 2020.
Sabon jirgin dai zai kasance yana dauke da wasu kamanni na Bae 146, wanda ke dauke da ingina hudu, sabon jirgin kuwa zai dinga samar da wutar da zai dinga aiki da ita da kanshi, a duk lokacin da yake sararrin samaniya.
Inda ita kuwa farfelar jirgin zata samar da wuta ga sauran kananan ingina uku dake taimakama jirgin. Kamfanin kera jirage na kasashen turai Airbus suke da alhakin kera wannan jirgin, tare da samun gudunmawa daga sauran kamfanonin biyu.
Facebook Forum