Hukumar kula da cinikayyar albarkatun man fetur ta Najeriya (NMDPRA) ta fara rabon lasisin cinikin iskar gas ga dillalan da suka cancanta a bangaren, sakamakon yawatar durkushewar babban layin lantarki na kasar.
An samu durkushewar layin lantarkin sau daya ne tak a sabuwar shekarar da muke ciki bayan da ya durkushe fiye da sau 10 a 2024, abin da ya jefa sassan Najeriya da dama cikin duhu na sa’o’i masu yawa.
Sanarwar da sashen yada labarai na NMDPRA ya fitar a yau Litinin dauke da sa hannun Jamilah Adama, yace al’amarin ya dace da umarnin Shugaba Bola Tinubu na tabbatar da cewa dukkanin tashoshin samarda lantarki na samun iskar gas din da suke bukata domin karfafa aikin fadada tsarin rarraba lantarkin da ake da shi a halin yanzu.
Sai dai hukumar ta gargadi dukkanin dillalan su tabbatar da dorewar samar da iskar gas kamfanonin samar da lantarkin ko kuma a soke lasisin nasu kasancewar ba za’a lamunci ayyukan zagon kasa ba,” kamar yadda sanarwar ta kara da cewa.
Dandalin Mu Tattauna