Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lalata Wayoyin Da Aka Birne Kusa Da Fadar Shugaban Kasa Ya Jefa Unguwannin Abuja Cikin Duhu -TCN


Wutar lantarki ta katse a duk fadin kasar Najeriya
Wutar lantarki ta katse a duk fadin kasar Najeriya

Wannan satar za ta haddasa rashin wuta a unguwannin Maitama, Wuse, Jabi, Life Camp, Asokoro, Utako da Mabushi.

Hukumar rarraba wutar lantarki ta Najeriya TCN tace wasu sun sace wayoyin layin rarraba wutar lantarkin karkashin kasa na 132kV dake baiwa tsakiyar Abuja da wasu unguwanni.

Mai magana da yawun hukumar ta TCN Ndidi Mbah ya fadi haka a wata takardar manema labarai da ya fitar yau Juma’a inda yace “a yankin gurin hutawa na Millenium Park da ke kusa da fadar shugaban kasa ta Aso Villa ne masu satar suka sace mita arba’in na abinda ke rarraba wuta na XLPE conductors.”

Ya kara da cewa wannan satar za ta haddasa rashin wuta a unguwannin Maitama, Wuse, Jabi, Life Camp, Asokoro, Utako da Mabushi.

Sanarwar tace tuni injiniyoyi na aiki don ganin an gyara tare da dawo da wutar a wadannan unguwanni da abin ya shafa.

~Alhassan Bala ~

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG