Babbar Manajar sashen hulda da jama'a Misis Ndidi Mbah ce ta bayyana haka a wata sanarwa da ta sa hannu kuma ta raba wa manema labarai.
Mbah ta ce za a dauke wutar ne saboda aikin gyaran hanyoyin da hukumar raya babban birnin tarayya (FCDA) ta ke yi a yankin Unguwar Apo.
Mbah ta ce aikin zai shafi turakun wuta mai girman kilowat 132 da mai Kilowat 33 ta hanyar layin Kukwaba zuwa Apo, sannan kuma mai kilowat 132 ta babbar hanyar kudancin birnin taraiyya.
Mbah ta lissafa yankunan da abin ya shafa da suka hada da Kubwa, Karu, Maraba, Nyanya, Masaka, Keffi, Kukwaba, da kuma Unguwar Makanikai ta Apo.
Har ila yau, gyaran layin wutar zai kuma shafi sassan Unguwar Lugbe da Unguwar Trademore da Pyakasa, har zuwa Sabon Lugbe, Chika da Alaita.
Sanarwar ta kara da cewa “Wannan babban aiki ne na sake tsugunar da turken wutar lantarki da zai sa a dauke wutar daga ranar 6 zuwa 20 ga watan Janairu, daga karfe 9 na safe zuwa 4 na yamma a kowache rana.”
Kamfanin TCN ya ba da hakuri kan wannan tsawon lokaci da za’a dauke wuta a wadannan Unguwanni tare da fatan idan an gama gyaran za’a samar da wutar lantarki mai yawa zuwa tashar wuta ta Apo daga tashar wutar lantarki ta Gwagwalada, wanda zai sa unguwanin su samu wutar lantarki babu tsinkewa.
Dandalin Mu Tattauna