Ministan Lantarki, Adebayo Adelabu, yace Najeriya ta kama hanyar kara megawat 150 kan babban layin lantarkin kasar kan nan da karshen shekarar 2024.
Adelabu ya bayyana hakan ne a yau Alhamis yayin ganawa da manema labaran fadar shugaban kasa bayan wata ganawar sirri da shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier da takwaransa na Najeriya Bola Tinubu a fadar ta Aso Villa dake Abuja.
A cewarsa, za a samu karin lantarkin ne sakamakon nasarar kammala kashin farko na shirin samar da lantarki na shugaban kasa (PPI).
“Mun yi amanar cewa kafin karshen shekarar da muke ciki, za a samu karin wutar lantarki mai karfin megawat 150 da zarar an kammala kashin farko na ilahirin shirin.”
Kalaman ministan na zuwa ne a dai dai lokacin da babban layin lantarkin Najeriyar ke rushewa a karo na 12 cikin wannan shekara, abin da ya jefa milyoyin gidaje cikin duhu.
Dandalin Mu Tattauna