Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tallafin Samar Da Lantarki A Najeriya Ya Karu Zuwa N199.64bn A Disamban 2024 - NERC


Ma'aikata na gyara a wasu turakun wutar lantarki a Najeriya (Hoto: X/TCN)
Ma'aikata na gyara a wasu turakun wutar lantarki a Najeriya (Hoto: X/TCN)

Rahoton ya nuna cewa gwamnatin tarayyar ta bar farashin lantarkin a yadda yake ga dukkanin rukunonin masu amfani da wutar.

Yawan kudaden tallafin da gwamnatin tarayyar Najeriya ke zubawa wajen samar da lantarki ya karu zuwa Naira biliyan 199.64 a watan Disamban 2024, a cewar bayanan da aka samo daga hukumar kayyade farashin lantarki ta Najeriya (NERC).

A cewar rahoton da aka fitar tallafin wutar lantarkin ya karu da kaso 2.76 cikin 100 zuwa Naira biliyan 199.64 a watan Disamban da muke ciki daga Naira biliyan 194.26 da ya kai a watan Nuwamban da ya gabata.

NERC ta kara da cewa, karin da aka samu a harkar musayar kudade da ta kayyade farashin dala a kan Naira 1, 687.45 da karuwar hauhawar farashi zuwa kaso 33.9 cikin 100, da kuma sauye-sauyen da aka samu wajen samar da lantarkin ne suka sabbaba samun dan karin.

Rahoton ya nuna cewa gwamnatin tarayyar ta bar farashin lantarkin a yadda yake ga dukkanin rukunonin masu amfani da wutar.

A yayin da rukunin kwastomomin dake kan damarar “A” suka ci gaba da biyan Naira 209 a kan kowane kilowat na lantarkin, an amince farashin da kwastomomin dake kan damarar “E” za su biya ya tsaya a yadda yake a watan Disamban 2022.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG