Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami’an Tsaro Sun Kubutar Da Fasinjoji 17 Da Aka Yi Garkuwa Dasu A Katsina


Wata majiyar soji ta bayyana  cewar an samu nasarar kubutar da mutanen ne sakamakon samun wani kiran gaggawa a ranar 11 ga watan Mayun da muke ciki, da misalin karfe 12 rana.

Rundunar jami’an tsaro ta hadin gwiwa ta kubutar da wasu fasinjoji 17 galibinsu maza daga hannun ‘yan ta’adda a shiyar Solar dake karamar hukumar Batsarin jihar Katsina.

Wata majiyar soji ta bayyana cewar an samu nasarar kubutar da mutanen ne sakamakon samun wani kiran gaggawa a ranar 11 ga watan Mayun da muke ciki, da misalin karfe 12 rana.

Majiyar ta kara da cewar nan take aka tura tawagar Rundunar Sojin Najeriya ta 9, da hadin gwiwar Rundunar ‘Yan Sandan jihar Katsina da dakarun sintiri na jihar da kungiyoyin mafarauta zuwa wurin da al’amarin ya faru.

Da isar tawagar jami’an tsaron, suka shiga zazzafar musayar wuta tsakaninsu da ‘yan ta’addar, inda nan take suka fatattakesu zuwa dajin dake kusa tare da barin mutanen da suke garkuwa dasu.

Majiyar sojin ta kuma bayyana cewar an samu nasarar kubutar da ilahirin fasinjojin da aka yi garkuwa dasu kuma tuni aka mika su ga jami’an karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina.

A sanarwar daya fitar a jiya Lahadi, sakataren yada labaran gwamnan katsina, Ibrahim Kaula Muhammad ya bayyana cewar dakarun sojin da aka tura yankunan jihar Katsina na aiki tukura domin dakile miyagun laifuffuka tare da kiyaye rayukan mazauna jihar.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG