Rahotanni na cewa an yi nasarar kubutar da wasu daga cikin dalibai da ‘yan bindiga suka sace a Jami’ar Confluence da ke jihar Kogi a arewacin Najeriya.
Cikin wata sanarwa da ya fitar, Kwamishinan yada labaran jihar Kinglsey Fanwo, ya ce mafarauta da tare da hadin gwiwar jami’an tsaro ne suka kubutar da daliban.
Jami’in gwamnatin bai fadi yawan daliban da aka kubutar ba, amma Kakakin ‘yan sandan jihar SP Williams Aya ya fadawa gidan talabijin na Channels cewa dalibai 14 aka kubutar.
Da farko gwamnatin jihar ta ce dalibai 9 aka sace.
A ranar Alhamis wasu ‘yan bindiga suka kutsa jami’ar wacce ke Osara suka kwashi dalibai suka yi cikin daji da su.
Kwamishina Fanwo ya kara da cewa sai da mafarauta da jami’an tsaro suka yi musayar wuta da ‘yan bindigar kafin a yi galaba akansu.
Jaridar This Day ta ruwaito Fanwo yana cewa jami'an tsaro na ci gaba da farautar ‘yan bindigar domin ganin an sako ragowar daliban.
Batun satar dalibai a makarantun firaimare da sakandare da ma jami’o’i a Najeriya ba bakon abu ba ne musamman a arewaci.
‘Yan bindiga kan sace dalibai da dama su kutsa da su cikin daji har sai an biya kudin fansa kafin a sako su.
Satar mutane domin neman kudin fansa, babbar matsala ce a mafi aksarin jihohin arewa maso yammacin Najeriya.
Hukumomin kasar sun ce suna iya bakin kokarinsu wajen ganin sun shawo kan karshen wannan al’amari.
Dandalin Mu Tattauna