Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dangin Namtira Bwala Sun Maka Makarantar Lead British International A Kotu, Suna Neman Diyar Naira Milyan 500


Shigar da karar ya biyo bayan faifan bidiyon daya karade shafukan sada zumunda a ‘yan makonnin da suka gabata inda aka wasu dalibai suna cin zalin Namitra Bwala.

Dangin Namitra Bwala, dalibar kwalejin “Lead British International School” dake Gwarinpa, a birnin Abuja, sun maka makarantar a kotu.

Shigar da karar ya biyo bayan faifan bidiyon daya karade shafukan sada zumunta a ‘yan makonnin da suka gabata inda aka ga wasu dalibai suna cin zalin Namitra Bwala.

Haka kuma dangin dalibar na neman diyar Naira milyan 500, da neman gafara a jaridun Najeriya guda 2 saboda gazawar makarantar wajen sauke nauyin daya rataya a wuyanta na samawa ‘yarsu kyakkyawan yanayin neman ilimi.

Karar wacce aka shigar gaban Babbar Kotun Birnin Tarayya, Abuja, tace gazawar makarantar wajen hana cin zalin dalibar, tare da gaggauta sanarda iyayenta da kuma gudanar da bincike akan lamarin har sai da bidiyon afkuwarsa ya karade shafukan sada zumunta alhalin tana karkashin kulawar makarantar, ya tabbatar da cewar akwai sakaci.

Sun kuma bayyana fatan cewar karar zata samar da gagarumin sauyi tare da daukar matakan da suka dace wajen hana afkuwar makamancin hakan a makarantar a nan gaba.

Dandalin Mu Tattauna

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG