Rundunar ‘yan sandan ta dakatar da jami’an ‘yan sandan na musamman ne biyo bayan kafa wani faifan bidiyo da jami’an rundunar ‘yan sandan na SPY su ka yi a dandalin yayata gajerun hotunan bidiyo “Tiktok a ranar 3 ga Agusta, 2022.
A cikin sanar da ta fitar dauke da rattaba hannun kakakin shelkwatar rundunar ‘yan sandan CSP Olumuyiwa Adejobi, rundunar ‘yan sandan ta bayyana cewa, “Sufeto-Janar na ‘yan sanda, IGP Usman Alkali Baba, psc(+), NPM, fdc, ya yi gargadi mai tsauri kan amfani da inifom din ‘yan sanda ba bisa ka’ida ba, da aka kebe musamman domin amfanin jami’an ‘yan sandan Najeriya, da ke kan aiki. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da aka dakatar da wasu jami’an ‘yan sanda guda biyu ba tare da bata lokaci ba, sabili da saba dokar aikin ‘yan sanda ta shekarar 2020, da kuma ka’idojin ‘yan sandan Najeriya na daukar ma’aikata, da karin gima, da kuma ladabtarwa na bangaren aikin ‘yan sandan na musamman da ake kira SPY a takaice da Sufeto-Janar na ‘yan sanda ya kirkiro a shekara ta 2013.”Sanarwar ta kara da cewa, “an kafa wannan bangaren rundunar ‘yan sanda na SPY ne, da ya hada da dokar ‘yan sanda ta 2020, da kuma ka’idojin daukar ‘yan sandan Najeriya, da kara girma, da kuma labadtar da jam’ian ‘yan sanda na SPY na 2013 ne da nufin mara ayyukan jami’an ‘yan sanda na yau da kullun a duk lokacin da ma’aikatu, da cibiyoyin gwamnati da kuma kamfanonin da suka shafi wadansu kasashe, da Bankuna suka gabatar da bukata, suka kuma sami amincewa, zasu biya kudin horas da su da kuma daukar nauyin kula da jin dadin su na tsawon lokacin da ake bukatar su gudanar da aikin. Kamar yadda Sashe na 21-24 na Dokar 'Yan Sanda, 2020 ya tanada.”
Sanarawar ta kuma ambaci bangaren dokar kafa rundunar ta musamman da ya shafi tsarin amfani da kayan ‘yan sanda da jami’an da aka dakatar su ka saba, inda sanarwar ta da bayyana cewa, “Hakanan yana da mahimmanci a bayyana cewa, bisa ga tsari, sashe na 25 (2) (3) na dokar 'yan sanda, na shekara ta 2020 da ka'idojin daukar 'yan sanda, da kara girma, da ladabtar da 'yan sanda na musamman, SPY na shekara ta 2013, wanda Sufeto-Janar na 'yan sanda ya bayar, an haramtawa jami'an SPY da ke sama da matsayi na Mataimakin Sufeto na 'yan sanda sa kayan sarki yayin da su ke gudanar da aiki…dole ne su kasance a cikin irin rigar da aka amince da su, riga mai kalar toka mai rubutun “SPY” da kuma rubutu a kafada dauke da kalmar “SUPERNUMERARY”…
Sanarwar ta kara da cewa, “Jami’an da aka dakatar - Obaze Blessing mai lambar SPY 5709, da Obaze Emmanuella Uju mai lamba 5708, sun yi ado da kakin ‘yan sanda na al’ada wanda ya sabawa ka’idar aikin rundunar ‘yan sanda ta musamman SPY. Hakazalika daya daga cikinsu ta sa mukamin Sufeto na 'yan sanda wanda ya saba wa doka. Banda haka kuma, sun bayyana kansu a cikin faifan bidiyo da wasu faifan bidiyo a matsayin marasa da’a da kuma kwarewa, wanda ya saba wa ka'idar 'yan sanda da ta shafi amfani da kafofin sada zumnunta, ta wajen fifita arziki da aka samu ta hanyar da ba ta kamata ba, da kuma rashin kame kai da ya janyo mummunar suka daga jama’a.
Sanarwar ta kuma yi kira ga dukan jami’an ‘yan sanda na rundunar ta musamman, su kiyaye dokokin sau da kafa saboda za a dauki mataki mai tsauri kan jami’an da suka saba doka. Hakazalika rundunar ta ce, tana sake duba wasu batutuwan da suka shafi saba ka’idar aiki da ake zargin wadansu jami’an ‘yan sanda da aikatawa da nufin zartar da hukuncin da ya dace.
Jami’an ‘yan sandan da aka dakatar dai ‘yan’uwan juna ne wadanda suka dauki hankalin al’umma lokacin da aka sa masu tambarin wannan aikin, kafin fitar da hoton bidiyon ta hanyar yayata bidiyo na TikTok cikin kayan aikin ‘yan sanda da kuma suturar nikayya da ya karrada kafofin sada zumunta, wanda ya dauki hankalin rundunar ‘yan sandan.
Bidiyon ya ja hankali ainu da a dare daya suka sami mabiya sama da dubu hamsin. Tuni aka sauke wannan bidiyon a dandalin na TikTok .
Jiya Jumma’a kakakin shelkwatar rundunar ‘yan sandan Olumuyiwa Adejobi, ya sanar da dakatar da su ba tare da bata lokaci ba.
Nan da nan masu bin shafin twitter na rundunar suka maida martani kan daukar matakin,
"Ya yi daidai, na gode Baba Usman Akali"
"Rundunar 'yan sanda na bukatar garambawul"
Kawo yanzu, babu wani bayani dangane da makomar jami’an ‘yan sandan.
A watan da ya gabata, rundunar 'yan sandan Najeriya ta kori Richard Gele wani sifetan 'yan sanda da aka nuna a faifan bidiyo a kafafen sada zumunta yana yabawa da kuma bada hujjar karbar nagoro da wadansu jami'an 'yan sanda su ke yi a hannun jama'a.