A yayin harin, ana fargabar yiwuwar 'yan bindigar sun yi awon gaba da wasu dalibai da malamai wadanda izuwa lokacin hada wannan rahoton ba a iya tantance adadinsu ba.
Kwamishinan Tsaron Cikin Gida da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa a yau dinnan Litinin. Ya lura cewa makarantar firamaren da 'yan bindigar suka kai harin tana cikin karamar hukumar Birnin Gwari, wadda miyagu iri iri su ka sha kai wa hare hare a lokuta da dama a jihar ta Kaduna.
Wani bangare na sanarwar ya ce, “Gwamnatin Jihar Kaduna ta karbi rahoton tsaro ksn sace wasu dalibai da malamai a wata makarantar firamare da ke Rema, karamar hukumar Birnin Gwari.
“Gwamnatin jihar Kaduna a yanzu haka tana kan samun cikakkun bayanai kan ainihin adadin daliban da kuma malaman da aka bayar da rahoton cewa an sace su kuma za ta fitar da cikakken bayani da wurwuri.”
Idan ba a manta ba, wasu 'yan bindigar ma sun yi awon gaba da dalibai sama da 30 a ranar Alhamis lokacin da suka kai hari Kwalejin Gandun Daji ta Tarayya, Afaka da ke karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna.