Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Babu Duriyar Dalibai 39, ‘Yan Mujami’ar RCCG 8 Da Aka Sace A Kaduna


Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El Rufa'i
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El Rufa'i

Kwana 19 bayan da ‘yan bindiga suka sace daliban kwalejin ilimin kula da gandun daji da ke Kaduna, har yanzu ba a san wane hali suke ciki ba.

A ranar 12 ga watan Maris ‘yan bindiga suka yi awon gaba da daliban su 39, maza 23 mata 16 a kwalejin wacce ke garin Afaka a karamar hukumar Igaba da ke jihar ta Kaduna a arewa maso yammacin Najeriya.

‘Yan bindigar da suka kai harin, sun yi niyyar kwashe daliban da yawansu ya kusa 200, amma jami’an tsaro da suka yi musayar wuta da su, sun yi nasarar kubutar da mutum 180.

Kwana biyu bayan sace daliban, maharan sun saki wani bidiyo wanda ya nuna ana dukan daliban, yayin da suke neman gwamnatin ta kai musu daukin gaggawa.

Wasu daga cikin daliban Kaduna da aka kubutar
Wasu daga cikin daliban Kaduna da aka kubutar

“Muna kira ga gwamnati da ta zo ta cece mu, an ji wa mafi akasarinmu rauni, akwai wasunmu da suke da larura ta rashin lafiya.” Daya daga cikin daliban wanda aka nuna shi ya fada a bidiyon.

A karshen makon nan da ya gabata, wasu rahotannin suka ruwaito mutuwar daya daga cikin mahaifan daliban, wanda ya rasu sanadiyyar matsalar bugun zuciya.

A wani labari makamancin wannan, har yanzu masu garkuwa da mutane na ci gaba da rike ‘yan mujami’ar Redeemed Christian Church of God (RCCG) su takwas da aka sace, su ma a Kaduna.

A ranar Juma’a aka yi awon gaba da mutanen, wadanda suke kan hanyarsu ta zuwa Kafanchan kamar yadda kungiyar Kiristocin Najeriya ta CAN reshen jihar Kaduna ta tabbatar.

A ranar Lahadi reshen kungiyar matasan ta CAN, (YOWICAN) ya yi kira ga gwamnati da ta kubutar da mutanen cikin gaggawa.

A baya-bayan nan gwamnan jihar ta Kaduna, Malam Nasiru El Rufa’i, ya ce gwamnatinsa ba za ta yi sulhu da ‘yan bindigar ba, amma ta ce tana kokarin ganin yadda za ta kubutar da daliban da sauran mutanen da ake garkuwa da su.

Matsalar satar mutane don neman kudin fansa ta zama ruwan dare a Najeriya musamman a arewa maso yammacin kasar.

A baya-bayan nan, ‘yan bindiga sun sace daruruwan dalibai 279 a garin Jengebe na jihar Zamfara, da wasu daliban a garin Kagara na jihar Neja da kuma wasu a garin Kankara na jihar Katsina, amma duk daga baya an sako su.

XS
SM
MD
LG