Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 13 Tare Da Kona Gida 56 A Kaduna


Taswirar Kaduna da hoton bindiga.
Taswirar Kaduna da hoton bindiga.

'Yan bindiga dadi sun far wa kananan hukumomin Zangon Kataf, Chikun da Kauru na jihar Kaduna a hare-hare daban-daban, inda suka hallaka akalla mutum 13, da raunata wasu mutane 7 da kuma kona gida kimanin 56.

Kwamishinan sha'anin tsaro da ayyukan cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ne ya bayyana haka, ya na mai cewa, "‘yan bindigan sun hallaka wani mutum da ya dawo daga gonarsa tare da dan uwan sa a kauyen Gora Gan da ke karamar hukumar Zangon Kataf, sai dai dan uwan nasa ya samu damar arcewa daga inda lamarin ya faru da ran sa.

A want labari makamancin wannan kuma, ‘Yan bindiga sun far wa kauyen Kizachi dake karamar hukumar Kauru inda suka hallaka mutane akalla 10 tare da raunata wasu 4.

Karin bayani akan: Samuel Aruwan, jihar Kaduna, Nigeria, da Najeriya.

A yayin harin na kauyen Kizachi, ‘yan bindigar sun kona gidaje 56 da babura 16, tare kuma da kona ma’ajiyar amfanin gona bayan sun debi iya ran su.

Gidaje da ke ci da wuta.
Gidaje da ke ci da wuta.

Majiyoyi dai sun bayyana cewa an garzaya da mutanen da suka jikata zuwa asibiti domin ba su kulawa.

Haka kuma, wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki a kauyen Masaka dake karamar hukumar Chikun inda suka hallaka mutum daya tare da raunata wasu 2.

A garin Kurmin Kaduna dake karamar hukumar Chikun ma ‘yan bindiga sun kashe mutum 1 tare da raunata wani mutum na daban.

A ranar 17 ga watan Maris da mu ke ciki, Dakarun rundunar yanki na daya na sojin Najeriya, sun sami nasarar kubutar da wasu mutane 10 da ‘yan bindiga suka yi awon gaba da su a baya-bayan nan daga rukunin gidajen ma’aikatan filin tashi da saukar jiragen saman kasa-da-kasa na kaduna, kamar yadda kakakin rundunar sojin kasar, Burgediya Janar Mohammed Yerima ya bayyana.

Gwamnan Kaduna a yayin karbar mutanen da sojoji suka kubutar daga hannun 'yan bindiga.
Gwamnan Kaduna a yayin karbar mutanen da sojoji suka kubutar daga hannun 'yan bindiga.

Har yanzu dai, ba'a sami nasarar kubutar da gomman dalibai da aka sace daga kwalejin horar da harkokin noma da lamurran da suka shafi gandun daji ta gwamnatin tarayyya dake garin Afaka na karamar hukumar Igabi ba, inda iyayen yaran da dailai ‘yan uwan su suka gudanar da zanga-zangar neman gwamnatin jihar Kaduna ta kubutar da yaransu daga hannun ‘yan bindiga.

XS
SM
MD
LG