WASHINGTON, D.C. —
Gidado I Abdullahi, shine Maigarin Tsauri, ya ce garin na Tsauri wanda aka kafa a shekarar 1840 ya taba zama gari na biyu a daraja a masarautar Katsina kuma garin ya shahara a fannin ilimi da yaki a zamanin bayan. Hausawa, Fulani, da Bare-bari sune kabilun da aka sani a garin a cewarsa.
Basaraken ya kuma ce asalin sunan garin "Sauki" amma daga baya ya koma "Tsauri."
Saurari cikakken shirin wanda Abdurrahaman Kabir Jani ya gabatar.
Facebook Forum