Babban Bankin Najeriya (cbn) ya rage yawan harajin bada kariya ga intanet a hada-hada ta na’ura daga kaso 0.5% zuwa kaso 0.005% cikin 100 a sabon jadawalinsa na harkokin kudin na shekarar 2024 zuwa 2025.
“CBN zai ci gaba da tursasa biyan harajin dole na kaso 0.005 cikin 100 a kan dukkanin cinikayyar da bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi suka yi ta na’ura, a cewar dokar yaki da laifuffukan intanet, ta 2015.”
Harajin, wanda aka gabatar karkashin dokar yaki da laifuffukan intanet ta 2015, wacce aka sabunta a 2024, an kirkire shi ne domin tallafawa asusun yaki da laifuffukan intanet na kasa, da ofishin mashawarcin shugaban kasa akan harkokin tsaro ke gudanar da shi
Za’a caji kaso 0.005 cikin 100 a kan dukkanin cinikayyar da bankunan kasuwanci dana hada-hada tsakanin kamfanoni da bankunan da basa mu’amala da kudin ruwa da hada-hadar kudi ta na’ura da sauransu.
Dandalin Mu Tattauna