Matar shugaban kasar Amurka, Michelle Obama ta nuna farin cikin ta akan matasan da suka halarci taron da akayi jiya a Washington, a ci gaba da bitar da akeyi kan shirin kafafawa gwiwar matasan Afirka don zama shuwagabanin na gari.
Mrs. Obama tace makasudi wannan bitar shine tattauna batun ilimin mata, inda ta jaddada mahimmancin ilimin 'ya mace, da kuma tabarbarewar ilimin mata a kasashen duniya masamman a nahiyar Afirka.
Harma ta bada misali da sace dalibai fiye da dari biyu da 'yan bindiga suka yi a makarantar sakandaren Chibok a jihar Borno a Najeriya.
Tace zahirin gaskiya ba abubuwan kyautata ilimin mata ne kawai zasu taimaka ba saida canjin dabiu da wasu aladu dake dakile ci gaban mata.