Shugaban kasa Barak Obama, ya ummurci matasan Africka masu halarta shirin da shugaban ya bullo da shi na karfafa ma matasan Afrika gwiwa domin zama shugabanni na gari. Da su tabbatar da cewa sun aiwatar da abubuwan da suka koya domin ci gaban nahiyar Afrika.
Ya furta hakan ne a lokacin da ya ke yi wa matasan jawabi a birnin Washington. Yace hakan ya zama wajibi domin nan gaba su zasu jagoranci nahiyar Afrika.
Ya kara da cewa Amurka zata horar da matasa a Afrika, a fannonin kasuwanci, kimiya, da shugabanci, yace domin ya gamsu da sakamakon daya samu akan su daga malaman dake hulda da su.
Shugaba Obama yace, a mako mai zuwa zai karbi bakuncin shuwagabanin kasashen Afrika, inda zasu tattauna abubuwa da dama da suka hada da batun tsaro, kiwon lafiya, kasuwanci da kuma wutar lantarki.
Shugaban na Afrika ya kuma yi albishir din cewa a shekaru biyu masu zuwa za a gudanar da taron a nahiyar Afrika. A kasashe kamar Senegal, Afrika ta gudu, Kenya da kuma Ghana.