Hukumar ta yanke shawarar yin hakan ne domin dakile yaduwar cututuka a sansanin musamman cikin yara kanana.
Shugaban hukumar Dr. Danlami Araf Ruguje shi ya bayyana yin hakan. Yace ya zama wajibi su yiwa yaran allurar domin tsoron barkewar annoba domin wata da ta kamu da bakon dauro sun kaita babban asibiti. Sabili da haka suka dauki shawara nan take a yiwa yaran allurar rigakafi.
Dangane da taimakon da mutanen jihar Gombe suke bayarwa jami'in yace babu abun da zasu ce sai dai su yiwa Allah godiya domin irin hobasan da mutane suka yi. Mutane sun bada taimako fiye da tsammani.
Ranar sallah wasu sun samu sun tafi idi kana jiya za'a yanka masu shanu a dafa masu shikafa su ci.
Kamar yadda za'a yi tsammani yara a sansanin sun fi yawa. Wasu yara da aka zanta dasu sun ce sun gudo ne gada Damboa domin an koresu. A can suna makaranta amma yanzu ba sa zuwa.
Ga rahoton Sa'adatu Fawu.