Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a Biciki Gwamnatin Murtala Nyako


 Tsohon Gwamna Jihar Adamawa Murtala Nyako.
Tsohon Gwamna Jihar Adamawa Murtala Nyako.

Mukaddashi gwamna jihar Adamawa, yace zai binciki gwamnatin, Murtala Nyako.

Mukaddashi gwamna jihar Adamawa, Hon. Ahmed Umaru Fintiri, yace zai biciki gwamnatin, Murtala Nyako, akan zargin yin fachaka da kudaden jihar, kimanin Naira miliyan dubu tamanin da biyu.

Zargin da ‘yan bangaren Nyako suka musanta, shi dai mukaddashi gwamnan wanda wa’adi mulkinsa na watani uku ne kafi a gudanar da zaben cika gurbi yace ya dauki wannan mataki ne domin kawo gyara a jihar.

A nasu martanin bangaran Murtala Nyako, sun zargi mukaddashin gwamnan ne da aiwatar da abunda suka kira siyasar bata suna na biyan bukatun wasu mutanen boye.

Ahmed Sajo, kakakin Murtala Nyako, yace abun mamaki ne ace an kashe kudin da tun hawan gwamnatin Murtala Nyako ba’a same rabin kudin ba bale ace an kashe.

Shi kuwa Lamidon Adamawa, Dr. Muhammad Aliyu Mustapha, ya shawarci mukaddashin gwamnan da ya daina ji jita-jita domin ciyar da jihar gaba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:38 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG