A can Burundi ana sa ran shugaban kasar zai sake cin zaben shugaba karo na 3, yayinda ‘yan kasar ke kada kuri’a yau Talata a zaben da ‘yan adawa suka ki yi.
An dai cigaba da hidimar wannan zaben bayan watanni da aka kwashe ana zanga-zangar adawa da gwamnati da kuma yin kira ga kasashe akan shugaban ya koma gefe guda.
Masu suka sun ce bai cancanta shugaba Nkurunziza ya sake shugabancin kasar ba, amma kotun kundin tsarin mulkin kasar ta ce shugaban ya cancanta saboda ‘yan majalisa ne suka zabe shi, ba sauran jama’a ba a karon farko da yayi mulki.
Zanga-zangar da aka yi ta kai ga tashin hankali, ciki har da jin fashewar nakiyoyi da harbe-harbe a daren wata litinin a Bujunbura babban birnin kasar.
Sakatare Janar din Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya yi kira ga hukumomi da su tabbata an samar da tsaro da kuma kwaciyar hankali lokacin zaben, ya kuma yi kira ga duk jam’iyyun kasar da su koma kan teburin tattaunawa.
Masu bada shawara a Majalisar Dinkin Duniya na sa ido a zaben na yau Talata, wanda ya kunshi masu kada kuri’a miliyan 3.8. a kasar ta Burundi