Kasar Burundi ta dage zaben ‘yan majalisa da aka shirya yi gobe Juma’a amma bata ce komi ba akan zaben shugaban kasa da za’a yi a wata rana cikin wannan watan.
Gervais Abayeho wani mai magana da yawun shugaban kasar ya shaidawa Muryar Amurka Sashen Faransanci Na Kasashen Afirka cewa ko shakka babu ba za’a gudanar da zaben ba gobe Juma’a.
Yace hukumar zabe na nazari akan wata ranar da zata gudanar da zaben bisa ga umurnin shugabannin kasashen dake yankin.
Kasar Burundi dai ta fada cikin rikicin siyasa tun lokacin da shugaban kasar Pierre Nkurunziza ya bayyana aniyar sake tsayawa zabe a watan Afirilu yana neman wa’adi na uku.
Masu sukar lamirin shugaban suna zargin cewa neman wa’adi na uku ya karya kundun tsarin mulkin kasar wanda ya bada wa’adi biyu kawai.
Tun lokacin mutane suka shiga zanga-zanga a babban Birnin kasar Bujumbura suna taho mu gama da ‘yansanda lamarin da yayi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 20.
Ko shekaranjiya Talata sai da wani mutm ya rasa ransa a Buterere wani dan gari dake kusa da Bujumbura saboda gurneti da aka jefa.
Matar Ndayizeye Janvier Abdul dan shekaru 38 da gurnetin ya kasha tace yana barci ne akan gadonsa jifan ya sameshi.
Shaidun gani da ido sun fadawa Muryar Amurka Sashen Afirka Ta Tsakiya cewa suna ganin an kashe Abdul ne saboda yana cikin jam’iyyar hamayya ta National Liberation Forces.