Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za a Gudanar da Zabuka Cikin Lumana- Nkurunziza


Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza
Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza

Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza ya fadawa kasarsa cewa za a gudanar da zabubbuka dake tafe cikin lumana, ya kuma dage akan cewa rikicin da aka yi kwanan nan a Bujumbura babban birnin kasar, bai dace da halayan dukan ‘yan kasar ba, duk da cewa ana ci gaba da yin zanga-zanga.

Mr. Nkurunziza ya yi wannan jawabin ne a wani gidan talabijin din gwamnati a yammacin jiya Laraba yayin da ya ba da sanarwar cewa za a jinkirta yin zaben ‘yan majalisa da mako guda, wato zuwa ranar 5 ga watan Yuni ke nan saboda tashin hankalin da ake fuskanta.

A makon da ya gabata ne ‘yan adawa suka so su hambarar da gwamnatin shugaban yayin da ya je wani taron kasashen yankin a kasar Tanzania.

Ba a dai sami nasarar yin juyin mulkin ba amma ana ci gaba da samun tashe-tashen hankula.

A yau Alhamis masu zanga-zanga sun yi arangama da ‘yan sanda, inda suka jejjefesu da duwatsu yayin da su kuma jami’an tsaron suka yi amfani da barkonon tsohuwa tare da yin harbin kashedi a iska.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce harsashi ya taba akalla mutum daya kuma ta yiwu ma ya mutu.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG