Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Kasar Burundi Ke Gudanar da Zaben 'Yan Majalisar Wakilai


Shugaban Burundi Nkurunziza
Shugaban Burundi Nkurunziza

A Burundi mahukuntan kasar suna ci gaba da zaben wakilan majalisar dokokin kasar yau Litinin duk da cewa 'yan hamayya sun kauracewa zaben.

Majalisar Dinkin Duniya da kuma kungiyar hada kan kasashen Afirka sun soki lamirin zaben tare da nuna fargaba cewa ba za’a yi adalci a zaben ba.

An tsananta matakan tsaro a fadin Bujumbura babban birnin kasar, duk da haka anji harbe harben bindiga, da kuma akalla fashewar gurneti a birnin.

Sai dai babu rahoton ko akwai wadanda suka jikkata.

Sai dai an bada rahoton zaben yana tafiyar hawainiya, domin anga mutane kalilan ne kadai suka fito.

Wata kusar AU Nkosazana Dlamini Zuma ta bayyana damuwa kan abunda ta kira "mummunar yanayin siyasa da tsaro" a Burundi, daga nan tace wakilan kungiyar masu sa ido kan harkokin zabe ba zasu sa ido kan zaben da ake yau ba.

Madam Zuma tace kungiyar hada kan kasashen Afirka, da Majalisar Dinkin Duniya da kuma kungiyoyin yankin sun yi kira ga Burundi ta jinkirta zaben harda na shugaban kasa da aka shirya za'a yi a karshen watan Yuli.

Amma gwamnatin kasar ta ki. Tace Burundi tana fuskantar "wani yanayi mai sarkakiya a tarihinta", kuma duk wani rikicin siyasa zai haifarda "mummunar sakamako ga zaman lafiya da tsaro" a kasar da kuma yankiN baki daya.

Shawarar da shugaba Pierre Nkurunziza, na yin takara wa'adi na uku ya janyo juyin mulki da bai sami nasara ba cikin watan jiya, da kuma ci gaba da suka daga wadanda suke cewa yana keta sharadin tsarin mulkin kasar da ya kayyade shugaba yayi wa'adi biyu kacal.

XS
SM
MD
LG