Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dokar Jinkirta Zaben Kasar Burundi


Shugaban kasar Burundi, Pierre Nkurunziza.
Shugaban kasar Burundi, Pierre Nkurunziza.

Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza, ya saka hanu a wata doka, wadda za ta jinkirta gudanar da zaben ‘yan majalisu da na kananan hukumomi, har sai zuwa ranar biyar ga watan Yuni,bayan zanga zanga da yunkurin juyin mulki da kasar ta fuskanta a kwanan nan.

Shugaban hukumar zaben kasar Pierre Claver Ndayingagire, ya tabattar da hakan ga Sashen Faransanci na Muryar Amurka. Hakan na nufin an jinkirta zaben na ‘yan majalisu da kwanaki goma kenan, sai dai babu wani bayanin da ke nuna cewa ko za a jinkirta zaben shugaban kasar, wanda za a gudanar a ranar 26 ga watan na Yuni.

Dubban mutane ne suke ta zanga zanga a Bujumbura, babban birnin kasar, suna kira ga shugaba Nkurunziza da kada ya nemi yin tazarce. A jiya Talata, ‘yan sanda sun yi amfani da barkonon tsohuwa tare da duka akan masu zanga zangar, wadanda suka sha alwashin ba za su daina boren ba har sai shugaban ya canja matsayarsa.

Masu adawa dai sun ce burin na Nkurunziza ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar, sai dai shugaban da masu mara mai bayan sun ce, yana da hurumin ya sake tsayawa takara, domin ‘yan majalisu ne suka zabe shi a wa’adinsa na farko a shekarar 2005, ba masu kada kuri’a ba.

Akalla mutane 20 ne suka rasa rayukansu yayin da ‘yan sanda da masu zanga zanga suke artabu. A dai makon da ya gabata ne, Shugaba Nkurunziza ya kaucewa wani yunkurin juyin mulki, yayin da yake halartar wani taron kasashen yankin da ke tattauna rikicin siyasar kasar ta Burundi a Tanzania.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG