Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

BORNO: 'Yanbindiga Sun Kashe Mutane Takwas a Karamar Hukumar Asikra Uba


Gwamnan jihar Borno Ibrahim Shettima
Gwamnan jihar Borno Ibrahim Shettima

Yayinda ake kyautata zaton za'a dakile hare-haren 'yan kungiyar Boko Haram sai gashi suna zafafa kai hare-hare da tayar da bamabamai a koina cikin jihohin arewa maso gabas kodayaushe suka ga dama.

Rahotanni dake fitowa daga karamar hukumar Askira Uba na nuni da cewa wasu mahara sun kai hari a garin Maikadiri dake masarautar Uba inda suka hallaka mutane takwas tare da raunata wasu.

Cikin kwanakin nan ana yawan samun hare-hare a kauyuka inda maharan suka fi zuwa su hallaka mutane su kuma kwashe masu dukiya. A wannan shirin da suka kai a kauyen Uba maharan sun kwashe shanu fiye da dari biyar bayan sun hallaka mutane da suke fitowa daga addu'ar safe ta ranar Juma'a kamar yadda suka saba yi.

Malam Bamanga Usman daya daga cikin mutanen da suka tsira yace 'yan Boko Haram din sun shiga garin ne kamar karfe goma na safe akan babura guda bakwai. Sun ga mutanen sun tsaya bakin masallaci sai suka bude wuta. Sun tafi da motocin da baburan mutane tare da shanu masu yawa.

Jami'an tsaro da suka bisu basu kama kowa ba. Amma 'yanbindigan sun fadawa mutanen garin zasu dawo su maida garin toka, wato zasu kona garin ke nan. Yanzu duk 'yan garin sun zama 'yan banga.

Ga rahoton Haruna Dauda Biyu.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG