Masana harkokin tsaro da shugabannin addinai suna mayarda martani akan daga hedkwatar sojoji zuwa Maiduguri a kokarin shawo kan rikicin 'yan Boko Haram.
Mayarda hedkwatar zuwa Maiduguri daga Abuja na cikin manyan matakan da sabon shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya dauka game da yaki da 'yan Boko Haram.
Tsohon gwamnan soji na Kano Kanar Sani Bello yana cikin wadanda suka bayyana ra'yoyinsu. Yace idan ana yaki da 'yan ta'ada ba daidai ba ne a ce hedkwatar sojoji na kilimita dari biyar daga inda ake yakin. Kamata ya yi ace hedkwatar wadanda ke yaki tana kusa dasu. Ba dede ba ne ace mai bada umurnin yana can uwa nesa da mayakan. Saboda haka matakin da shugaban kasa ya dauka dede ne kuma sojojin kansu zasu ji dadi.
Shi ma sakataren kungiyar malaman masallatan juma'a a jihar Neja Imam Umar Faruk yace sun gamsu da matakin da shugaban kasa ya dauka. Yace da an yi haka ne tuntuni da an warware matsalar.
Tarzomar da kungiyar Boko Haram ta jefa yankin arewa maso gabas ciki, musamman jihar Borno ta gurguntar tattalin arzikin wurin. Wani dan kasuwa yace matakin da shugaban kasa ya dauka ya kwantar masu da hankali.
Ga karin bayani a rahoton Mustapha Nasiru Batsari.