Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Biden Ya Yi Wa Mambobin Kwamitin Majalisa Da Suka Binciki Trump Afuwa


Tsohon shugaban Amurka Joe Biden a US Capitol Rotunda na Washington, DC, Janairun 20, 2025. (Photo by SAUL LOEB / POOL / AFP)
Tsohon shugaban Amurka Joe Biden a US Capitol Rotunda na Washington, DC, Janairun 20, 2025. (Photo by SAUL LOEB / POOL / AFP)

Shugaba Joe Biden yayi afuwa ga Dr. Anthony Fauci da Janar Mark Milley mai ritaya da mambobin kwamitin Majalisar Wakilai da suka binciki harin da aka kaiwa Majalisar Dokokin Amurka na ranar 6 ga watan Janairu

Biden ya yi amfani da ikon musamman da mukaminsa ya bashi a sa’o’insa na karshe wajen basu kariya daga ramuwar gayya daga gwamnatin Trump mai shigowa.

Shawarar na zuwa ne bayan da Donald Trump yayi gargadin cewar jerin sunayen makiyansa na ciki da mutanen da suka ci amanarsa a siyasance ko kuma suka nemi a hukunta shi saboda yunkurinsa na sauya rashin nasarar daya gamu da ita a zaben 2020 da kuma rawar daya taka wajen kaiwa Majalisar Dokokin Amurka ta Capitol hari a ranar 6 ga watan Janairun 2021.

Rantsar da sabon Shugaban Amurka na 45 da 47, Donald Trump Janairun 20, 2025
Rantsar da sabon Shugaban Amurka na 45 da 47, Donald Trump Janairun 20, 2025

Trump ya zabi wadanda zai nada a mukamai a majalisar ministocinsa daga cikin mutanen da suka goyi bayan farfagandarsa kuma suka sha alwashin hukunta wadanda keda hannu a kokarin bincikarsa.

“Bai kamata ayi kuskuren fahimtar wannan afuwa da amincewa da cewar wani mutum ya aikata ba daidai ba, kuma bai kamata a yi tawilin amincewa da afuwar a matsayin yadda da aikata ba daidai ba,” kamar yadda Biden ya bayyana a cikin wata sanarwa.” Wadannan ma’aikatan hukuma na bin kasarmu dimbin bashin godiya saboda jajircewa ba tare da gajiyawa ba wajen hidimta mata.”

Rantsar da sabon Shugaban Amurka na 45 da 47, Donald Trump Janairun 20, 2025
Rantsar da sabon Shugaban Amurka na 45 da 47, Donald Trump Janairun 20, 2025

Al’ada ce shugaban kasa yayi afuwa a karshen wa’adin mulkinsa, saidai irin wadannan ayyuka na jin kai ana gabatar dasu ne ga gamagarin amurkawa da aka samu da laifin aikata laifuffuka.

Saidai Biden yayi amfani da ikon nasa ta fafadar hanyar wacce ba kasafai ake amfani da ita ba: wajen yiwa mutanen da ba’a kai ga bincika ba afuwa. Kuma ana kallon amincewa da hakan tamkar amsa cewa sun aikata laifi ne, duk da cewar a hukumance ba’a tuhumi mutanen da aka yiwa afuwar da aikata wani laifi ba.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG