A can baya shugaban kasar dan jam'iyyar Democrat ya ce ba zai yafe wa dansa ko kuma ya sassauta hukuncin da aka yanke masa ba, bayan yanke masa hukunci a shari'o'i biyu a jihohin Delaware da California.
Wannan matakin dai na zuwa ne 'yan makwanni kafin Hunter Biden ya fuskanci hukuncinsa, bayan da aka tabbatar masa da laifi na sha’anin bindiga, da kuma amsa laifi da yayi kan abin da ya shafi haraji, kuma kasa da watanni biyu kafin zababben shugaban Amurka Donald Trump ya koma fadar White House.
An kwashe dogon lokaci ana shari'ar ta ɗan shugaban kasar, wanda ya fito karara ya bayyana cewa ya fuskanci binciken gwamnatin tarayya a watan Disamban shekara ta 2020, wata guda bayan nasarar Joe Biden a shekarar ta 2020.
A watan Yuni ne Biden ya yanke shawarar cewa ba zai yi wa dansa afuwa ba, inda ya fada wa manema labarai cewa dansa na fuskantar shari'a akan bindiga a Delaware, ya ce "Zan amince da hukuncin da masu taya alkali yanke hukunci suka yanke. Ya kara da cewa zan yi hakan kuma ba zan yi masa afuwa ba.
Dandalin Mu Tattauna