Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yi alkawarin daukan dawainiyar karatun wata matashiya da ya yi wa afuwa bayan da ta kwashe shekara bakwai a gidan yari sanadiyyar kashe mijinta da ta yi.
“Gwamna ya dauki alkawarin zai kula da iliminta da makamantansu, saboda shawarar da ita hukumar gidan ajiya da gyaran hali ta bayar na cewa mutuniyar kirki ce, tun da ta zo ba a samu matsala da ita ba.” In ji kakakin hukumar kula da gidajen daurarru da gyaran halin ta Najeriya shiyyar Kano, DSP Misbahu Lawan
Shekarun Rahma Hussain 13 da haihuwa kuma tana aji 3 na makaranatar firaimare a lokacin da aka yi mata aure.
“Wannan kwamiti na shugaban kasa da suka zo suka kai ziyara ga mai girma gwamna, inda suka nemi gwamna da ya kalli wannan yarinya saboda an yi mata aure ne na dole kuma yarinya ce karama tana da buri a ryuwarta. Alhamdulillahi gwamna ya yi mata afuwa aka kuma yafe mata.” Lawan ya kara da cewa.
Rahma Hussaini wacce a banan nan ne ta cika shekaru 20 daidai da haihuwa ta nanata godiya ga gwamnan Kano.
“Mai girma gwamna na gode, na gode Allah ya saka da alheri, Allah ya raba ka da kujerarka lafiya. Kuma na ji ka yi min alkawari da makaranta, Allah ya ba ka ikon iyawa, na gode Allah ya saka da alheri.” Ramha ta ce cikin hawaye yayin hirar da Muryar Amurka ta yi da ita.
A 2014 babbar kotun Kano ta yanke hukunci kisa ga Rahma bayan samun ta da laifin kashe mijinta ta hanyar soka masa wuka a cikin sa.
Sai dai Rahma Hussini ta fadawa kotu a lokacin cewa, yi mata auren dole ne ya sanysa ta sokawa mijin nata wuka a ciki kuma ya mutu.
Bayan sauraron shari’ar kusan tswon shekaru 4, a shekara ta 2018 ne alkalin kotun mai shari’a R.A Sadik ya yanke mata hukuncin kisa, amma tare da danka hurumin yi mata afuwa a hannun gwamna, la’akkari da karancin shekarun ta da kuma yanayin tursasa mata auren dole.
Sai dai shekaru 3 bayan wannan hukunci, gwamnan na Kano ya amince da shawarwarin kwamitin shugaban kasa kan yiwa daurarru afuwa dana hukumomin kula da gidajen daurarru na Kano, inda a juma’ar nan Rahma Hussaini ta shaki iskar ‘yanci.
Baya ga Rahama Hussaini, wasu daurarru dake da nauyin bashi a wuyansu da wadanda suka tsufa da kuma masu fama da rashin koshin lafiya, duka sun ci gajiya tsarin afuwar, a wani mataki da hukumomin Najeriya ke dauka na rage cunkoso a gidajen yarin kasar.
Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari: