Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Biden Ya Yi Jawabi Mai Sosa Rai


Shugaban Biden a babban taron jam'iyyar Democrat
Shugaban Biden a babban taron jam'iyyar Democrat

Alamu sun nuna cewa Biden ya dan zubar da hawaye a lokacin da ya hau dandamalin da ya yi jawabin inda aka kwashe sama da minti hudu ana sowa da nuna masa kyakkyawar tarba.

Shugaban Amurka Joe Biden ya gabatar da jawabinsa a babban taron jam’iyyar Democrat a daren Litinin yana mai cewa ya yi iya bakin kokarinsa a shugabancin kasar.

Biden ami shekaru 81, ya samu gagarumar tarba makonnin bayan da wasu da yawa daga cikin ‘yan jam’iyyarsa suka matsa masa ya janye takararsa ta neman wa’adi na biyu.

Wata guda bayan da Biden ya janye takarar tasa, an tsara gangamin na Chicago a matsayin wani dandali na yin ban-kwana da shi.

Kazalika taron wani dandali ne namika akalar tafiyar da jam’iyyar ta Democrat ta dukufa wajen hana tsohon shugaban Amurka Donald Trump dawowa a wa’adi na biyu.

Dakin babban taron jam'iyyar Democrat a Chicago
Dakin babban taron jam'iyyar Democrat a Chicago

A ranar Litinin, Biden ya yi karin haske kan rade-radin da ake yi cewa yana jin haushi don an matsa masa ya janye – duk da cewa akwai rahotanni da suka nuna akasin hakan inda ya yi kira ga ‘ya’yan jam’iyyar da su marawa Harris baya.

“Na tafka kurakurai da dama a rayuwata ta siyasa, amma iya bakin kokarina na yi.” Biden ya ce.

Biden wanda ya yi jawabin nasa cikin annashuwa da kakkausar murya inda ya kare ayyukansa.

Biden da Kamala Harris a Chicago,
Biden da Kamala Harris a Chicago,

Jawabin nasa na daren Litinin, ya tunawa jama’a shekarar 2020 da Biden ya lashe zabe inda yake magana ba tare da tangarda ba sabanin yadda akan gani yana magana da kyar a baya-bayan nan, kamar yadda aka gani muhawarar da suka yi da Trump.

Alamu sun nuna cewa Biden ya dan zubar da hawaye a lokacin da ya hau dandamalin da ya yi jawabin inda aka kwashe sama da minti hudu ana sowa da nuna masa kyakkyawar tarba.

Biden ya kuma yi kira ga jama’a da su nuna cikakken goyon baya ga mataimakiyarsa Kamala Harris wacce ya kwatanta a matsayin wacce za ta iya kare muradun Amurka.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG