Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Taron Democrat: Kamala Harris Ta Yi Jawabin Ba-zata


Harris Chicago
Harris Chicago

Fitowa da yin jawabi ba zato ba tsammani da Mataimakiyar Shugaban Amurka kuma 'yar takarar shugaban kasa, Kamala Harris, ta yi a babban taron jam'iyyar Democrat na daya daga cikin jerin abubuwan da su ka burge jama'a a daren farko na taron na kusan mako guda.

Yayin da dinbin ‘yan jam’iyyar Democrat ke sauraro da kallon raye raye da kade kade da kuma jawaban sharar fage a babban taron jam’iyyar da aka fara da daren jiya Litini a birnin Chicago na jahar Illinois ta Amurka, sai kwatsam, Mataimakiyar Shugaban kasar Amurka, kuma ‘yar takarar shugaban kasar jam’iyyar, Kamala Harris, ta bayya ta kuma hau kan mumbarin kafe, sai kawai aka barke da sowa ta murna; ana jinjina ma ta.

Ta na karbar makiraho sai ta ce ma babban taron, “Barka da dare kowa da kowa.” Aka sake barkewa da sowa. Ta sake cewa, “Barka da dare, barka da dare. Abin farin cike ne kasancewa da kowannenku a wannan daren, a wannan dandalin da kuma sauran jama’a da ke gida. Wannan makon zai zama gawurtacce.” Sai aka sake barkewa da sowa ta murna.

Bayan nan, sai Kamala ta ce, za ta so farawa da jinjina ma “shahararren shugabanmu, Joe Biden, wanda zai yi jawabi nan gaba a wannan daren.” Sai ta kara da cewa, “Joe mun gode da shahararren salon shugabancinka a tsawon rayuwar da ka yi ka na bauta ma kasarmu, da kuma duk abubuwan da za ka ci gaba da yi. Mu na masu godiya gare ka har abada.” Sai dandanlin taron ya sake barkewa da matukar sowa ta murna da yabo ga Joe Biden.

Kamala ta ci gaba da jawabi da cewa yayin da ta ke kallon kowa a wannan taron, babu abin da ta ke gani illa kawai kyawun kasarmu mai girma. Ta ce mutane sun zo daga kowani sashi na kasarmu da kuma bangarori daban daban na rayuwa sun hallara a nan saboda fata iri guda da su ke da shi game da makomar kasar. Don haka a watan Nuwamba mai zuwa “za mu hada kai mu ayyana da murya guda a matsayin al’umma guda cewa, mu fa mikewa za mu yi gaba.”

Ta ce da kwarin giwa, fata na gari da kuma imani sannan “tare da irin kaunar da mu ke ma kasarmu, kasancewar mun san cewa abubuwan da su ka hada mu sun fi abubuwan da su ka raba mu, bari mu tashi tsaye don jaddade abubuwan da mu ke muradi. Kuma a ko yaushe mu tuna cewa a duk lokacin da mu ka yi gwagwarmaya mu kan yi nasara.”

Ga jawabin na Kamala Harris a Turance:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:07 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG