Mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris ta zabi gwamnan jihar Minnesota Tim Walz a matsayin wanda zai zama mata mataimaki a zaben shugaban kasa.
Wasu mutane uku da ke da cikakkiyar masanaiya kan lamarin ne suka tabbatarwa da Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press a ranar Talata.
Walz, wanda Gwamna ne mai ci kuma tsohon soja, ya taka muhimmiyar rawa wajen kare ‘yancin zubar da ciki.
A tarihi, babu wani dan takarar shugaban kasa daga jam’iyyar Republican da ya taba lashe jihar Minnesota ba tun bayan shekarar 1972, amma Donald Trump da gangamin yakin neman zabensa ya ce za su lashe jihar a wannan karon.
Walz ya shiga gangamin yakin neman zaben na Harris ne a wani lokaci mai sarkakiya a tarihin siyasar Amurka.
Kusan daukacin ‘yan jam’iyyar Republican sun nuna goyon baya ga Trump bayan da aka yi yunkurin halaka shi a watan Yuli.
Makonni kadan bayan hakan, Shugaba Joe Biden ya janye takararsa, lamarin da ya sa Harris ta karbi ragamar tafiyar da jam'iyyarsu ta Democrat musamman wajen hada kan ‘ya'yanta.
Dandalin Mu Tattauna