Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Za Ta Aikawa Ukraine Tallafin Soji Na Dala Miliyan 125


Tallafin zai kumshi makamai da karin kayan aiki, wanda zai kasance kunshin tallafi na 10 da Amurka ta aika zuwa Ukraine, tun lokacin da shugaba Joe Biden ya rattaba hannu kan dokar tallafawa tsaron Ukraine a watan Afrilu.

A ranar Juma’a, Amurka ta ba da sanarwar cewa za ta aike da tallafin soji na dala miliyan 125 zuwa ga Ukraine, wanda ya hada da makamai masu linzami na da na'urorin kariya, biyo bayan mutuwar fararen hula da dama sakamakon wani sabon harin da Rasha ta kai.

Tallafin zai kumshi makamai da karin kayan aiki, wanda zai kasance kunshin tallafi na 10 da Amurka ta aika zuwa Ukraine, tun lokacin da shugaba Joe Biden ya rattaba hannu kan dokar tallafawa tsaron Ukraine a watan Afrilu.

Amurka ta amince da tallafin dala biliyan 175 da za’a aika wa Ukraine tun bayan da Rasha ta mamaye kasar a watan Fabrairun shekara ta 2022, a cewar Majalisar Harkokin Waje, wata kungiya mai zaman kanta da ke New York.

Sanarwar tallafin ta zo ne sa'o'i bayan harin makami mai linzami da Rasha ta kai kan wani babban kanti a garin Kostiantynivka, wanda ya kashe akalla mutane 14 a Ukraine tare da raunata wasu kusan 44.

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya rubuta a dandalin sada zumunta na X cewa "Rasha ce ke da alhakin wannan ta'addanci." Har kawo lokacin hada wannan rahoto Rasha ba ta ce uffan ba akan harin.

Jami’an agajin gaggawa na aikin nemo wadanda suka tsira da watakila suke binne a karkashin baraguzan ginin, a cewar Zelenskyy. An bayar da rahoton barna ga shaguna, gidaje, motoci da kuma ofishin gidan waya da ke yankin.

Sanarwar ta sake tabbatar da goyon bayan Amurka ga Ukraine sannan ta ce Amurka "za ta tura wannan sabon taimako cikin gaggawa don karfafa tsaron Ukraine na yankinta da al'ummarta."

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG