Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bude Babban Taron Jam'iyyar Democrat


Harris & Walz
Harris & Walz

Jiga jigan 'yan jam'iyyar Democrat sun fara jawabai a babban taron jam'iyyar da za a shafe wajen mako guda ana yi a birnin Chicago na jahar Illinois ta nan Amurka.

Kamar yadda aka al’adanta, an bude babban taron na Democrat ne tare da jawabai, sakwanni da matsayar 'yan deliget daga wurare daban-daban kan tsayar da ‘yar takarar ta shugaban kasa da mai mara mata baya.

Tsohuwar ‘yar takarar shugaban kasa ta jam’iyyar a zaben shekara ta 2016 Hillary Clinton, na daga cikin jiga-jigan jam’iyyar da suka gabatar da jawabai a ranar ta farko, inda ta mai da hankali kan halaye, dabi’u da kwarewar da suka sa ‘yar takarar jam’iyyar Kamala Harris ta fi cancanta da shugabancin kasar.

Ta ta’allaka fafutukar ta Harris da gwagwamaryar da ta yi a matsayin ta na mace, tana mai cewa su biyun sun nuna irin yadda mata a Amurka suke gwagwarmaya wajen samawa al’umma ‘yanci.

Clinton wadda ta sha kaye a hannun Donald Trump na jam’iyyar Republican a zaben na 2016, a cikin jawabin na ta, ta caccaki Trump din da ke neman wa’adin mulki na 2 a zaben na bana, musamman kan manufofin sa da ta bayyana a matsayin na biyan bukatun kai a maimakon kasa, a lokacin wa’adin mulkinsa na farko.

Ta ce “labarin rayuwa ta da tarihin kasar mu shine, ana iya samun ci gaba. To amma ba tabbas, dole sai mun yi fafutukar samun nasarar, kuma babu gajiyawa. A ko wane lokaci akwai zabi. Shin za mu yi gaba ne ko kuma mu dawo baya?”

Hillary Clinton matar tsohon shugaban kasar Amurka Bill Clinton, wacce ta yi aiki a matsayin sakatariyar harkokin wajen Amurka a lokacin mulkin Barrack Obama, ta amince tare da bayyana goyon bayanta ga takarar Kamala Harris tun ranar da Shugaba Joe Biden ya bayyana janyewarsa daga takara, tare da nuna goyon bayansa ga mataimakiyarsa.

Jawabin shugaban kasa Joe Biden ne ya rufe zaman taron na farko, inda ya jaddadada cewa matsayarsa ta janyewa daga takarar zaben tana da nasaba da kishin kasa da kuma kare muradun kasa.

A rana ta 4 kuma ta karshe ne ake sa ran Kamala Harris ta yi jawabin amincewa da tsaida ita takarar shugaban kasa, amma kuma kafin nan, manyan shugabanni za su gabatar da na su jawaban, ciki dar da tsohon shugaban kasa Barrack Obama, da ma dan takarar mataimakin shugaban kasa, Tim Waltz.

A saurari rahoton Murtala Sanyinna:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:48 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG