Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hamas: Abin Da Amurka Ta Ce Kan Nada Yahya Sinwar


Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken
Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken

A ranar Talata kungiyar ta Hamas ta sanar da nada Yahya Sinwar a matsayin sabon shugabanta bayan kisan Isma'il Haniyeh a Iran da ake zargin Isra'ila na da hannu.

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ce sabon shugaban Hamas da aka zaba Yahya Sinwar yana da ikon ganin an cimma yarjejeniyar dakatar da bude wuta a yakin Isra’ila da Hamas a Gaza.

Kungiyar mayakan Falasdinawa a ranar Talata ta zabi Sinwar, babban jami’inta a Gaza wanda ya shirya farmakin 7 ga Oktoba a Isra'ila, bayan an kashe shugaban kungiyar Ismail Haniyeh a ranar 31 ga Yuli a Iran a harin da ake zargin Isra’ila ce ta kai.

Sabon shugaban Hamas, Yahya Sinwar
Sabon shugaban Hamas, Yahya Sinwar

Fargaba a yankin Gabas ta Tsakiya ta ƙaru bayan kisan Haniyeh, wanda Iran ta ɗora wa Isra'ila laifi, kuma an sa rai za ta mayar da martani. An kuma nuna damuwa sosai bayan da Isra'ila ta kashe wani shugaban Hezbollah a Lebanon mako na baya.

A kokarin da kasashe ke yi, Shugaban Amurka Joe Biden ya yi magana da Shugaban Masar Abdel Fattah El-Sisi a ranar Talata game da kokarinsu na an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.

Firaiminsitan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya gaya wa majalisar zartarwarsa cewa, Isra’ila a shirye take ta gwabza fada da Iran da dukkan mukarrabanta

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG