Yakin da aka shafe watanni da ana ta yaki ya jefa dubban daruruwan Falasdinawa a yankin da aka yi wa kawanya a cikin matsananciyar yunwa, inda sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ce a yanzu haka kowa da kowa a Gaza na bukatar agajin jin kai.
Wani kiyasi da Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar ya ce mutane 300,000 a yankin arewacin kasar za su fuskanci matsananciyar yunwa nan da watan Mayu idan ba a samu karin agaji.
Babban jami'in kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya Volker Turk ya ce Isra'ila na katse hanyoyin agaji tare da gudanar da yakin ta hanyar da "ka iya kaiwa ga amfani da yunwa a matsayin hanyar yaki".
Sojojin Isra'ila a ranar Talata sun ci gaba da kai farmaki kan babban asibitin Gaza, wanda suke zargin ana amfani da shi wajen aikin soji.
A martanin da ya mayar, shugaban Hamas na Qatar Ismail Haniyeh ya zargi Isra'ila da neman "tayar da hargitsi da ci gaba da tashin hankali" da kuma "yin zagon kasa ga tattaunawar da ake yi a Doha".
"Ayyukan da sojojin yahudawan Sihiyoniya suke yi a rukunin gine ginen asibitin
sun tabbatar da aniyarsu ta kawo cikas ga farfadowar rayuwa a Gaza da kuma wargaza muhimman al'amuran rayuwar bil'adama." In ji Haniyeh
Hakan dai ya zo ne a daidai lokacin da aka sake komawa kan teburin shawarwarin tsagaita bude wuta a Qatar, bayan da aka kasa cimma yarjeniya bayan shafe makwanni ana tattaunawa domin ganin an sasanta watan Ramadan mai alfarma da aka fara a makon jiya.
Mummunar yakin Gaza da ba a taba irinsa ba ya barke ne bayan wani harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba wanda ya yi sanadin mutuwar mutane kusan 1,160 ‘yan Isra'ila, galibi fararen hula, kamar yadda wani alkaluman jami'an Isra'ila na AFP ya nuna.
Isra'ila ta mayar da martani da kai farmaki kan Hamas wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 31,819, yawancinsu mata da kananan yara, a cewar ma'aikatar lafiya ta Gaza.
Blinken, wanda zai je Saudiyya da Masar a wannan makon don kokarin samar da goyon baya ga tsagaita wuta na wucin gadi da kuma karuwar agaji, ya bayyana cewa kowa a Gaza yana fama da matsananciyar karancin abinci.
Shugaban Amurka Joe Biden na matsin lamba ga Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da ya ja da baya daga wani gagarumin farmakin kasa da yake barazanar yi.
Sai dai Netanyahu ya ce ya gaya wa Biden cewa "mun kuduri aniyar kammala kawar da wadannan bataliyoyin a Rafah, kuma babu yadda za a yi a yi hakan ba tare da kutsawa daga ta kasa ba".
Tuni dai aka kai hare-haren bam a birnin, inda gidan talabijin na AFP ya nuna yadda mazauna garin ke bincikan baraguzan gine-gine don neman abinci a ranar Talata bayan wani harin da aka kai a daren.
Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya kuma yi taho mu gama cikin dare, inda da yawa daga cikin matsugunansu ba su da inda za su gudu sai tantuna na wucin gadi.
Oum Abdullah Alwan ta ce ‘ya’yanta sun yi kururuwar tsoro saboda “ba za mu iya banbance karar ruwan sama da karar harsasai ba”.
Jami'ai sun bayyana a watan Janairu cewa an ruguza tsarin kwamandojin Hamas a arewacin Gaza.
Amma harin da aka kai wa Al-Shifa ya sake mai da hankali a arewancin kasar.
Isra'ila ta dade tana zargin mayakan da yin amfani da asibitoci a matsayin sansanoni kuma a baya sojoji sun kai farmaki kan Al-Shifa a watan Nuwamban bara, lamarin da ya janyo cece-ku-ce a duniya.
Dandalin Mu Tattauna