Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bana Bakwai


Bana Bakwai
Bana Bakwai

Shirin Bana – Bakwai na wannan satin ya sami jin salon Magana ne daga wani matashi wanda yace a nasu yankin yawanci matasa na amfani da Kalmar ‘yan kwallo wato own goal a turance, wannan kalma dai na nufin idan dan wasan kwallo ya jefa kwallo a ragar gidan su, wato ya ci gida Kenan.

Dan haka a duk lokacin da wani ke kan maganar wani ko gulma alhali kuma shima yana da irin wannan matsala, zaka ji wadanda ke wurin sunce ‘OWN GOAL” ma’ana dara ta ci gida Kenan.

Daga karshe ya kara da cewa yawancin samarin da ke shaye shaye kuma sukan yi amfani da Kalmar ‘LAWA”, yace da zarar kaji sun fadi wanna kalma, tojami’an tsaro suka hango. DAWAREWA kuma na nufin tserewa.

Saurari cikakkiyar hirar a Danadlivoa.com

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG